Gwamnatin Jihar Neja ta ba da umarnin hana motocin da suka fito daga Maje hawa gadar Dikko.
Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya ba da umarnin a lokacin da ya ziyarci wurin da wata tankar mai ta yi gobara a mahadar Dikko da ke karamar hukumar Gurara ta jihar Neja.
Gwamnan, wanda ya koka kan yadda wasu direbobi ke nuna halin ko-in-kula yayin tuki, ya ce ba a amince duk wata mota da ta fito daga Maje ta bi ta gadar Dikko ba, sai dai su bi karkashin gadar zagayo kan hanyarsu.
Ya kuma umurci babban kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya da ya kafa rundunar tsaro a yankin domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni, yayin da ya yi kira ga kungiyoyin sufuri da abin ya shafa da su ba hukumar kiyaye hadurra ta kasa hadin kai.
Sai dai Gwamnan ya bayyana fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a matsayin abin tausayi tare da gode wa Allah da lamarin bai kai ga al’ummar da ke makwabtaka da su ba.
Umar Bago ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakin kammala aikin titin Minna zuwa Suleja domin jinkirin aikin hanyar yana haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Gwamnan ya godewa Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, da Hukumar Kashe Gobara, da Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, da Kungiyar Sufuri ta Kasa (NURT) da sauran hukumomin da suka bayar da gudunmawa wajen kawo dauki ga wadanda fashewartankarya rutsa da su.
Ya ce za a kara tura likitoci daga asibitocin da ke Minna domin su taimaka wajen kula da wadanda suka jikkata da ke samun kulawa a babban asibitin Suleja.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj