Akwai sauran rina a kaba! Duk da gwamnoni sun amince da ƙudurin dokar haraji –  In ji Ndume

FB IMG 1737211108792

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya ce amincewar da kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi kan kudirin dokar haraji abin a yaba ne amma bai wadatar ba saboda har yanzu akwai wasu sassan kudurorin da ke bukatar karin haske.

Ndume, wanda ya yi shura wajen sukar wasu manufofin gwamnati mai ci, ya ci gaba da cewa, maimakon gyara, gyaran harajin zai kara dora wa talakawa nauyi, inda ya bukaci shugaban kasa ya janye kudirin.

Da ya ke magana a wata hira da Sashen Hausa na BBC, Ndume ya ce, “Abin da gwamnonin su ka yi abu ne mai kyau, amma bai isa ba saboda har yanzu ba mu da cikakkiyar fahimta kan kudirin.”

Ya kara da cewa, duk da cewa matakin na NGF mataki ne da ya dace, akwai bukatar a bude kofofin tuntuba da shawarwarin jama’a domin a samu matsaya daya a kan dokar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *