Gwamnatin Nijeriya ta kama mutane 327 bisa zargin harkar ma’adanai ta ɓarauniyar hanya

FB IMG 1742650684030

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta kama mutum 327 da ake zargi da aikin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin ƙasar.

Alfijir labarai ta rawaito cewa Ministan Ma’adanai Dele Alake ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a bikin cika shekara ɗaya da kafa rundunar kula da harkokin haƙar ma’adanai ta Mining Marshals (MM).

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito shi yana cewa an kama mutanen ne tun daga kafa rundunar a 2024 sun yi nasa, inda ma’aikatarsa ta yi nasarar gurfanar da 143 daga cikinsu a gaban kotu.

Ya ƙara da cewa babban abin da suka saka a gaba a 2025 shi ne gurfanar da sauran mutanen a gaban shari’a.

An ƙaddamar da rundunar MM ne ranar 21 ga watan Maris na 2024, inda ta fara aiki da dakaru 2,220 kafin su ƙaru zuwa 2,670, a cewar NAN.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *