Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Sallah Babba A Kasar

Alfijr

Alfijr ta rawaito gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun babbar Sallah don Bikin Eid-ElKabir.

Litinin 11 da Talata 12 ga Yuli, 2022, a matsayin ranakun hutu don bikin Eid-el-Kabir na bana.

Alfijr

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar Musulmi da ‘yan Nijeriya na gida da kuma na kasashen waje murnar wannan rana.

“Ina kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da haɗa soyayya da zaman lafiya da kyautatawa da sadaukarwa kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da su da kuma amfani da wannan lokacin wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da hadin kai da wadata da kwanciyar hankali. na kasar nan, duba da irin kalubalen rashin tsaro da muke fuskanta a halin yanzu,”

Kamar yadda Aregbesola ya bayyana a cikin sanarwar

Slide Up
x