Gwamnatin Tarayya Ta Yi Rabon Tallafi Ga Kananan ‘Yan Kasuwa A Jigawa

Screenshot 20240724 152115 Facebook

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya yi wannan kiran a lokacin kaddamar da ayyuka daban-daban da ofishinsa ya jagoranta wanda aka gudanar a dandalin Malam Aminu Kano Triangle da ke  Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Alfijir labarai ta ruwaito Shettima ya yi nuni da cewa, da wuya irin wadannan ayyuka za su haifar da ci gaba mai kyau kuma za su iya haifar da tashin hankali da lalata dukiyoyin al’umma.

Kashim Shettima bayyana cewa, gwamnati mai ci a karkashin Bola Ahmed Tinubu tana aiki tukuru wajen aiwatar da manufofi da shirye-shirye da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa bullo da tsare-tsare masu inganta rayuwar al’ummar Jigawa.

A nasa jawabin gwamna Umar Namadi ya bayyana ziyarar mataimakin shugaban kasar a matsayin cigaba da kuma amfani ga al’ummar jihar Jigawa.

“A yau, Mataimakin Shugaban kasa ya kaddamar da asibitocin MSME don inganta harkokin kasuwanci da bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu”.

Gwamnan ya ce mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kuma kaddamar da shirin noman rani da ke amfani da hasken rana mai fadin hekta 20,000.

Sauran ayyukan sun hada da kaddamar da samar da wutar lantarki mai karfin hasken rana KVA 100 domin samar da tsayayyen wutar lantarki ga masu kananan sana’o’i a kasuwannin Dutse, da kaddamar da shirin horas da matasa 1,000 daga jihar Jigawa kan fasahar kere-kere”.

Namadi ya kara da cewa, ci gaban kananan masana’antu, kanana da matsakaitan masana’antu shi ne jigon ajandar sabunta fata, da ke da nufin samar da yanayin da ya dace da ci gaban tattalin arziki mai dunkulewa da dorewar ci gaban tattalin arziki, wanda a karshe zai fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci.

“Muna farin ciki da cewa wannan ya yi daidai da Ajandarmu ta  Jigawa, inda muke shirin aiwatar da tsare-tsare masu da nufin tallafawa da inganta harkokin kasuwanci, da bunkasa kananan ‘yan kasuwa.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *