Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shari’ar da ta ke yi wa mai kiran #REVOLUTIONNOW, Omoyele Sowore kan zargin cin amanar kasa.
Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwar dakatarwar babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Alhamis mai dauke da sa hannun babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) a jiya Larabar da ta gabata, ta ce mai shigar da kara (Gwamnatin Najeriya) za ta dakatar da shari’ar.
Sanarwar ta ce, “Saboda ikon da aka bani a karkashin sashe na 174 (1) (c) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, sashe na 107 (1) na Hukumar Shari’ar Laifuka ta 2015 da duka. Ni Lateef Olasunkanmi Fagbemi, SAN, na dakatar da tuhumar mai lamba FHC/ABJ/CR/235/2019.
Idan zaku tuna a ranar Larabar da ta gabata cewa Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya sake yin barazanar soke tuhume-tuhumen da ake yi na cin amanar kasa da ake zargin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaben 2019 da 2023, Omoyele Sowore. idan har gwamnatin Najeriya ba ta shirya ci gaba da shari’ar ba bayan shekaru biyar.
Alkalin ya yi gargadin ne a ranar jiya Laraba a ci gaba da sauraron karar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V