Hakeem Baba-Ahmed Ya Kunno Wuta: “Tinubu Ya Gaji Bashi Da Kuzarin Gyaran Najeriya”

IMG 20251201 WA0079

Daga Aminu Bala Madobi

Cikin wata hira da manema labarai, Tsohon mashawarci na musamman kan siyasa a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Dr. Hakeem Baba-Ahmed, kuma tsohon kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Northern Elders Forum (NEF) ya kwanto kura.

Cikin kalaman da ya furta, Hakeem Baba Ahmad ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai da karfin ci gaba da jagorantar Najeriya, balle har yayi yunkurin sake neman kujerar a 2027.

Baba-Ahmed, wanda ya sauka daga mukaminsa na Mai bada Shawara Na Musamman Kan Siyasa a ofishin Mataimakin Shugaban Kasa a watan Afrilu, ya yi tankade da rairaya a shirin Sunday Politics na Channels TV inda ya ce:

“Tinubu ba bashida wani kuzarin gyara kasar nan. Ba shi da kwarin gwiwar da zai fitar da Najeriya daga halin da take ciki.”

Ya kara da cewa duk wata “hikima ko basira” da ake cewa shugaban ya zo da ita lokacin yaƙin neman zabe a yanzu ta ki bayyana a aikace — tattalin arziki yana tangal tangal, tsaro ya tabarbare, talaka ya tagayyare, komi sai addua.

Dr. Baba-Ahmed yace “Idan APC na son cigaba, su nemo matashi ko sabon jini mai kuzari. Tinubu ya koma gefe.”

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *