Hasashen yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimaka Ko Akasin Wajen Shigar Dalibai Jami’a a Najeriya

IMG 103343 161025 1760607236643

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cire wajibcin shiga makarantun gaba da sakandare a fadin kasar, wanda a baya darasin lissafi da turanci wajibi ne sai da shi ake samun gurbin shiga wadannan makarantun.

Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai.

Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba. 

Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin fasaha, kimiyya da injiniya. Wannan ya sa ake tambaya ko cire lissafi daga wajabcin shiga manyan makarantu ba zai iya rage ingancin dalibai a nan gaba ba.

Menene Ra’ayin ku?

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *