Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila, akalla Falasɗinawa uku sun rasa rayukansu a ranar Alhamis sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza, in ji majiyoyin lafiya a yankin.
Wata hukumar gwamnatin Isra’ila ta ce zai yi wuya ta buɗe iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar don zirga-zirgar mutane.
Tuni dai Ministan tsaron Isra’ila ya umarci rundunar sojin kasar da ta yi kwakkwaran shiri don murkushe Hamas muddin ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar.
A nata bangaren, Hamas ta mayar da gawarwakin wasu Isra’ilawa biyu da ta kama, amma ta amince cewa tana bukatar kayan aiki na musamman da taimako don gano sauran gawarwakin da ke cikin baraguzan gine-gine.
Ya zuwa yanzu, yakin Isra’ila a Gaza ya kashe akalla mutane 67,967 tare da jikkata 170,179 tun daga Oktoba 2023.
A Isra’ila kuma, mutane 1,139 ne suka mutu a harin ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, kuma aka kama kimanin 200.
Aminiya
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t