Jagoran matasan jam’iyyar ADC a jihar Kano, Hon. S.A Saminu Shehu Isyaku Kura, ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da ma ‘yan Najeriya baki ɗaya da su fito su yi rajista a jam’iyyar (ADC) domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.
Hon. Kura ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai da kuma shigar jama’a cikin harkokin siyasa domin samar da canji mai ma’ana a ƙasar.
Ya ce lokaci ya yi da matasa da sauran al’ummar Najeriya za su taka rawar gani wajen zaɓen shugabanni nagari ta hanyar shiga jam’iyyun siyasa da kuma yin rijista a jam’iyyar da suke ganin za ta kawo ci gaba ga ƙasa.
A cewarsa, jam’iyyar ADC tana da kyakkyawan tsari da manufofi da za su taimaka wajen kawo cigaba a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma, musamman a bangaren tattalin arziki, ilimi da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.
Hon. Kura ya kara da cewa matasa su ne ginshikin kowace al’umma, saboda haka yana da muhimmanci su kasance a sahun gaba wajen gina makomar Najeriya ta hanyar shiga siyasa da kuma bada gudummawarsu wajen tabbatar da shugabanci nagari.
Ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da wayar da kan jama’a a kan muhimmancin yin rijista da kuma goyon bayan jam’iyyar ADC domin samun nasara a zaben 2027.
A ƙarshe, ya jaddada cewa idan aka haɗa kai tare da goyon bayan jama’a, jam’iyyar ADC za ta iya zama wata babbar karfi a siyasar Najeriya a zaɓen da ke tafe.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t