Hukumar Abuja Ta Rusa Gidaje Dubu Sha 15 Da Aka Gina Ba Bisa Ƙa’ida Ba

FB IMG 1707948265729

Hukumar kula da birnin tarayya Abuja, ta rusa gidaje sama da 15,000 na haramtattun gidaje da gidajen kwana a gundumar Gwarinpa da ke babban birnin tarayya Abuja

Alfijir labarai ta rawaito daraktan da ke kula da ci gaban birnin tarayya Abuja, Muktar Galadima, ne ya bayyana haka ya yin ganawarsa da manema labarai a lokacin da ake gudanar da aikin rushe gidajen, ya bayyana cewa, haramtattun gine-ginen sun rufe titin arterial Road (N16), wanda ya taso daga Sakatariyar Gwamnatin Tarayya, ta nufi hanyar Maitama da Katampe zuwa Jahi, sannan ta dangana zuwa Gwarinpa.

Galadima ya bayyana cewa sashen da ke kula da taswira na Hukumar FCTA a shirye yake ya fara aikin titin da zarar an kammala rusa ginin, kuma tuni aka bayar da aikin gina hanyar.

“Wannan wurin da muke kan titin titi ne, titin arterial ne da ake kira N16, amma a daya bangaren titin kuma yana hade da titin da ake kira Titin Shehu Shagari. Don haka, yana farawa ne daga Sakatariyar Tarayya, ta hanyar Maitama da Katampe da Jahi zuwa Gwarinpa.

“Kamar yadda na ce, wadannan gine-gine ne da aka gina ba bisa ka’ida ba a kan titin. Shi ya sa za mu zo mu cire su domin Sashen kula da taswira za su fara aikin nan take. Don haka ya zama dole mu kawar da gine-ginen da ke hana su aikin gina titinan.

“Muna da mutane sama da 10,000 zuwa 15,000 da ke zama a nan wurin ba bisa ka’ida ba. Kamar yadda muke sharewa a yanzu, masu aikin suna kan jiran aiki, wanda tuni an bayar da kwangilar aikin. ” in ji shi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *