Hukumar CAC za ta fara farautar wasu masu sana’ar POS a Najeriya

FB IMG 1765035167008

Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC) ta bayyana cewa za ta fara cafke dukkan masu gudanar da ayyukan na’urar biyan kuɗi (POS) da ba su yi rajista ba daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar,  ta bayyana yawaitar na’urorin POS da ba su yi rajista ba a matsayin “aiki babu ka’ida” wanda ya saba wa dokokin Companies and Allied Matters Act (CAMA) na 2020 da kuma ka’idar aikin dillalan banki ta Babban Bankin Najeriya (CBN).

“Wannan aiki marar ka’ida, wanda wasu kamfanonin fasaha na kuɗi ke taimakawa, na iya jefa tsarin kuɗin Najeriya da dukiyar jama’a cikin haɗari. Wannan dole ne ya tsaya,” in ji CAC.

Sanarwar ta ƙara da cewa babu wani mai gudanar da POS da za a bari ya yi aiki ba tare da rajista a CAC ba, kuma hukumomin tsaro za su tabbatar da bin wannan umarni a faɗin ƙasar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *