Hukumar Hisba Tayi Amai ta Lashe! Kan Gayyato Sarauniyar kyau Shatu Garko.

 Bayan surutai da jama’a suka yi ta yi, hukumar Hisbah ta Kano ta musanta shirin gayyatar Shatu Garko 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Hukumar Hizbah ta Kano ta musanta rade-radin da ake yadawa na cewa hukumar za ta gayyaci Miss Nigeria, Shatu Garko, da iyayenta da aka yi kwanan nan domin halartar gasar kwalliya.

Jaridar Solacebase ta rawaito, babban Daraktan Hukumar Hizbah Dr. Aliyu Musa Kibiya ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano ranar Laraba. 

Idan za a iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne babban kwamandan hukumar, Haruna Ibn Sina, a wata hira da ya yi da  manema labarai, yayi Allah-wadai da halartar Shatu Garko a gasar Sarauniyar kyau, inda ya ce hakan ya saba wa koyarwar Musulunci da al’adun Arewa.

Best Seller Channel 

 Ya ce nan ba da jimawa ba za a gayyaci iyayenta domin su yi magana kan dalilin da ya sa suka ba ta damar shiga gasar. 

Mun yi bincike kuma mun tabbatar da cewa yarinyar mai suna Shatu Garko ‘yar jihar Kano ce kuma ‘yar asalin karamar hukumar Garko ta jihar Kano inda ita ma Hisbah ke aiki.

 Dakta Aliyu Musa Kibiya ya bayyana cewa hukumar Hizbah ba ta ce zata  gayyatar Shatu Garko ko iyayenta  domin amsa tambayoyi ba. 

Sai dai ya kara da cewa kwamandan ‘rundunar, Haruna ibn Sinai, a martanin da manema labarai suka yi masa, shi ne ya yi wa’azin adawa da gasar kyau, yana mai cewa laifi ne. 

Best Seller Channel 

Idan dai za a iya tunawa, Shatu Garko ta kafa tarihi inda ta zama mai hijabi ta farko da ta saka Miss Nigeria a lokacin da aka tabbatar da nasaraarta a makon jiya a Lagos. 

Slide Up
x