Yan Sanda 4 Sun Shiga Hannu Bisa Laifin Karbar Cin Hanci (Na Goro)

 Jami’an ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun kama wasu jami’an ‘yan sanda hudu da laifin karbar na goro (Kudi)

Best Seller Channel 

Best seller channel ta rawaito, wasu yan sanda hudu sun shiga hannun jami’an ‘yan sanda bisa zargin karbar kudi daga wani matafiyi a Abuja.

Best Seller Channel 

 Jami’an, wadanda ke aikin ababen hawa a area 11, an gansu a cikin wani faifan bidiyo suna karbar kudi daga wajen fasinjojin, wanda ba a iya tantance ko wanene su ba. 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ta ce kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Sunday Babaji, ya bayar da umarnin cafke jami’an tare da bincikar su cikin gaggawa. 

Sanarwar ta ce, “Rundunar ‘yan sandan na son yin kira ga duk wanda ke da hanyar tuntubar matashin a cikin bidiyon da aka karbatwa kudin da ya yi ya mika masa sakon gayyata ga jami’ar hulda da jama’a na rundunar. 

“Kwamishinan, wanda ya samu labarin cikin tsananin rudani, ya bayyana halayen jami’an a matsayin rashin mutunci, wani aiki da bai dace da dan sanda ba, kuma ya kauce ma ainihin kimar gaskiya da ake sa ran dan sanda dashi. 

Ya kuma bayyana cewa ba za a amince da irin wanna cin kashin ba da sunan aikin dan sanda, kuma ba za a yi kasa a guiwa ba wajen gudanar da matakin da ya dace.

Best Seller Channel 

” Kamen ‘yan sandan hudu na zuwa ne kwanaki biyu bayan da hukumar ‘yan sandan ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan wasu ’yan sanda da ake zargin wasu ’yan sanda sun yi wa wasu ’ karbar Naira miliyan 22 na Bitcoin a jihar Lagos 

Slide Up
x