Hukumar INEC Ta Amince da Sabbin Jam’iyyu 14 a Najeriya

FB IMG 1757754167093

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta amince da rijistar sabbin jam’iyyun siyasa guda 14, wadanda za su fara shiga sahun manyan ayyukan siyasa da zabuka a Najeriya.

INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, in da ta ce an karbi bukatun kungiyoyi 171 da ke neman rajista a matsayin jam’iyyu, sai dai daga cikin su, 14 ne kawai suka cika sharuddan da doka ta tanada.

A cewar hukumar, an gudanar da tantancewar bisa tanadin Sashe na 222 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, da kuma Sashe na 79 (1, 2 da 4) na Dokar Zabe ta 2022, wadanda suka bayyana sharuddan da kowace kungiya za ta bi kafin samun damar zama jam’iyyar siyasa a kasar.

“Daga karshe, kungiyoyi 14 ne suka cika ka’idar hukumar zaben, yayin da sauran kungiyoyi 157 suka gaza cika ka’idar,” in ji sanarwar INEC.

Sabbin jam’iyyun da hukumar ta amince da su sun hada da:

ATP,
ADA,
ANC,
ASP,
AAP,
CDA,
DLA,
GRIP,
GFP,
LPP,
NDP,
NRP,
PPA,
PFP.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *