Hukumar KNUPDA Ta Yi Gargadi Da Kwakkwaran Jan Kunne Game Da Gine-Gine A Jihar

Screenshot 20240429 104624 Facebook

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe

Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu ya saba wa sashe na 11,12 da 13 na dokar KNUPDA za a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Alfijir Labarai ta rawaito Ibrahim na cewar, gargadin ya zama wajibi ganin yadda ake samun karuwar gine-gine ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba. Ya kuma bukaci jama’a da su samu takardar izinin gini daga KNUPDA kafin su fara kowane irin gini.

Architect Ibrahim ya yi nuni da cewa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta saukaka hanyoyin samun takardar izinin gini a jihar.

“Kwanan nan an samarda wata na’ura da za ta gaggauta ba jama’a takardar izinin gini ba kamar da a da sai an dauki watanni kafin a kammala aikin.” Sai dai ya jaddada cewa masu neman izinin gini su kuma gabatar da zane kafin zuwa neman iznin don kwaucewa rugujewar gini a nan gaba.

Manajan daraktan ya lissafo jerin matakan da KNUPDA ta dauka don tabbatar da cikakken bin al’umma.

Ya bayyana abin takaicin da ya faru a baya-bayan nan a matsayin sakaci domin tun da farko KNUPDA ta ba su takardar su dakatar da aikin ta daya da ta biyu kafin ginin ya ruguje.

Architect Yakubu Adamu ya kuma bayyana cewa an gudanar da tarurruka tare da hadin gwiwar jami’an tsaro domin gano wanda ya gina shi tare da gurfanar da shi.

Architet Ibrahim ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rigamu gidan gaskiya tare da addu’ar Allah ya wadanda suka sami rauni lafiya.

RM

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *