Hukumar NAFDAC Ta Garƙame Shagunan Masu Magani A Kano

IMG 20240218 124715

Daga Amina magaji Muhammad

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta rufe fiye da shaguna guda ɗari bakwai na masu sayar da magunguna a yankin Malam Ƙato da ke jihar.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar NAFDAC ta kulle shagunan ne a daren jiya Asabar ta hanyar ƙara musu mukullai tare da liƙa takardu a jikinsu da suke nuni da cewar sune suka kulle shagunan.

Da ya ke zantawa da manema labarai, shugaban hukumar mai kula da shiyyar Kano Ƙasim Ibrahim, ya ce, sun ɗauki matakin kulle shagunan ne a ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa, masu sayar da magungunan sun bi doka ta hanyar komawa kasuwar magani ta Dan-gwauro.

“Akwai ƙarin shaguna da za a samar a kasuwar sakamakon ƙorafin wasu masu sayar da maganin da ke cewa rashin wurin zama ne ya hana su komawa, “in ji Kasim”.

Shugaban hukumar mai lura da shiyyar Kano Ƙasim Ibrahim, ya ƙara da cewa, za su ci gaba da kulle shagunan masu sayar da magungunan da suke zaune ba bisa ƙa’ida ba har zuwa lokacin da suka cimma dai-daito.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *