Hukumar NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawarta Ta Shekarar 2022

Alfijr ta rawaito Mahukuntan hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO sun fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2022.

Alfijr Labarai

Da yake sanar da sakamakon jarrabawar a garin Minna ta jihar Neja a ranar Alhamis, magatakardar hukumar ta NECO, Farfesa Dantani Wushishi ya ce, masu ruwa da tsaki sun amince da gudanar da aikin na shekarar 2022.

Wushishi ya bayyana cewa mutane 1,209,703 ne suka yi rijistar jarabawar tare da maza 636,327 wanda ke wakiltar kashi 52.60 da mata 573,376 wanda ke wakiltar kashi 47.39 cikin 100.

Shugaban NECO, ya ce 1,198,412 ne kadai suka zana jarrabawar da maza 630,180, wanda ke wakiltar kashi 52.58 cikin 100 da mata 568,232, wanda ke wakiltar kashi 47.41.

Alfijr Labarai

Yawancin wadanda suka zana jarrabawar masu buƙatu na musamman 1,031, tare da raguwa kamar haka: 98 tare da albinism, 177 masu fama da Autism, 574, masu nakasar jiki, da 107.

“Yawancin wadanda da suka ci Credit a cikin Harshen Ingilishi 889,188 suna wakiltar kashi 74.89 cikin 100

Waɗanda da suka ci Credit kuma a lissafi sune 929,140 wanda ke wakiltar kashi 78.23 kamar yadda sanarwar ta gabata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *