Hukumar Yaki Da Cutar Kanjamau Ta Wayar Da Yan Kannywood A Kan Cutar

Best Seller Channel 

KSACA ta wayar da kan Kannywood akan yaki da cutar kanjamau ta hanyar fim

Best Seller Channel 

 Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (SACA), ta shirya taron wayar da kan jama’a na kwana daya a ranar Lahadi, domin karfafa wa masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood kwarin gwiwa kan bayyano batutuwan da suka shafi cutar kanjamau a harkar fim.

 KANO FOCUS ta ruwaito cewa Darakta Janar na Hukumar, Sabitu Shu’aibu Shanono, ya dora wa masu shirya fina-finai aikin bincike kafin su fara fina-finan da suka shafi lafiya. 

Ya bayyana cewa masu shirya fina-finan Kannywood na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen bayar da shawarwari, domin suna da dimbin jama’a a cikin al’umma. 

Shugaban ya umarce su da su ba da gudummawar tasu don ganin karshen cutar, don haka akwai bukatar a gabatar da yaki da cutar yadda ya kamata. 

A cewar sa, “Lokaci ne da masu fama da cutar ke mutuwa cikin sauki kamar yadda har yanzu ake gabatarwa a fina-finan mu na Kannywood.” 

Ya kuma shawarce su da su nemi karin haske kan muhimman al’amura daga hukumar kafin fara fina-finan da suka shafi cutar kanjamau. 

Sai dai shugaban hukumar ya jaddada shirin hukumar na kulla kyakkyawar alaka da masana’antar, da kuma samar da muhimman bayanai ga masu shirya fina-finai. 

Shi ma da yake nasa jawabin, Babban Sakatare na Hukumar Tace Tace na Kano, Ismail Na’abba Afakallahu, ya yabawa hukumar kan wayar da kan jama’a. 

Ya bayyana rawar da masu shirya fina-finai ke takawa wajen wayar da kan muhimman batutuwa musamman kiwon lafiya. 

Afakallah ya yi kira da a hada kai tsakanin masana’antar da hukumar, domin aikewa da jama’a bayanan da suka dace. 

Best Seller Channel 

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar Motion Pictures Association of Nigeria (MOPPAN), Kabiru Maikaba, ya bukaci a ci gaba da tallafa wa irin wadannan hukumomi. 

Ya kuma jaddada bukatar wayar da kan masana’antar Kannywood da bayanan da suka dace domin ciyar da masu sauraronsu. 

Kabiru Maikaba ya yi alkawarin bawa kungiyarsa goyon baya, wajen bayar da gudunmuwar kawo karshen cutar, kamar yadda suka yi a wasu fannoni. 

Best Seller Channel 

Shahararriyar marubuciyar nan ta Hausa kuma mace ta farko mai shirya fina-finai, Hajiya Balaraba Ramat a lokacin da take magana, ta tuno da wasu cece-kuce da ake samu a auren masu dauke da cutar kanjamau. 

“Amma a yau, mun ga canji a wannan yanayin saboda mutanen da ke dauke da kwayar cutar sun yi nasarar yin aure har ma suna da yara,” in ji ta. 

Ta dorawa hukumar alhakin ci gaba da wayar da kan jama’a domin a Koda yaushe masana’antar a shirye take domin yin gyara da ilimantarwa, cikin nishadantarwa. 

Fitaccen marubucin Kannywood, Ado Ahmad, ya bayyana wasu daga cikin gudunmawar da marubucin Hausa ke bayarwa wajen wayar da kan jama’a game da shekarun farkon cutar kanjamau a Kano. 

Ya ce masana’antar adabin Hausa da Kannywood sun taimaka sosai wajen yada labarai.

Best Seller Channel 

Slide Up
x