Daga Abdu Ado K/Naisa
Shugaban Hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi gami da kwacan waya na jihar Kano, Brigadiar General Gambo Mai Aduwa (Mai ritaya) yayi holin wasu matasa guda hudu ga manema labarai, wadanda hukumar ta kama a kano.
Alfijir Labarai ta rawaito Mai Aduwa ya ce hukumar ta kama matasan a gurare da ban-dabam bisa zargin su da aikata miyagun dabi’u wadanda suka jibanci sha da sayar da miyagun kwayoyi gami da kowacen waya.
Kamar yadda yai karin haske, mutum biyu an kama su bisa zargin sai da muggan kwayoyi da kuma tabar wiwi, daya kuma yana sayar da maganin gargajiya wanda aka hadashi da madarar sukudaye da kuma farar kwaya wadda akewa lakabi da( sha fara Kaga Aljan).
Haka kuma shugaban ya ce guda biyu daga cikinsu ana zargin su da kwacan waya, sai dai daya ya barranta kansa da hakan, inda ya ce shi “Dan sane” ne kawai.
Gambo ya bukaci iyaye da sauran jama’a da su taimakawa kokarin gwamnatin na magance wanna matsala da ta Addabi al’umma gami da sanar da hukumarsa irin wanna batagari cikin hanzari.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj