Ibtila’i! Ƴan Bindiga Sun Kashe Sojoji 16 A Jihar Delta

Screenshot 20221027 112452 com.android.chrome edit 10136481627099

Wasu matasa sun yi kwanton ɓauna tare da kashe sojoji, ciki har da hafsoshi 16 na bataliyar 181 ‘Amphibious Battalion” dake aikin samar da zaman lafiya a yankin Okuoma dake karamar hukumar Bomadi a jihar Delta a ranar Alhamis.

Alfijir labarai ta rawaito wadanda aka kashe dai sun hada da kwamandan rundunar, Manjo biyu, Kyaftin daya da sojoji 12.

Darakta mai rikon kwarya na yada labarai na tsaro, Brig.-Gen. Tukur Gusau ne ya bayyana haka a yau Asabar a Abuja.

Ya bayyana cewa an yi wa sojojin kwanton bauna ne tare da kashe su a lokacin da suke kan hanyar kashe wani rikici da ya taso tsakanin kabilun Okuama da Okoloba a Delta.

Mista Gusau ya bayyana cewa babban hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da cafke wadanda ke da hannu a wannan danyen aikin.

Ya kara da cewa an kai rahoton lamarin ga gwamnatin jihar Delta.

“Sojoji, duk da haka, sun ci gaba da mai da hankali da kuma jajircewa kan aikinsu na wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

“Ya zuwa yanzu, an kama wasu ‘yan kadan yayin da ake daukar matakan gano musabbabin harin,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *