Ibtila’i! Adadin Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Kyandar Biri A Najeriya Ya Kai 53 – In Ji NCDC

Rigakafi

Kusan makonni biyu da suka gabata Amurka ta ba Najeriya allurar rigakafin cutar ta kyandar biri

A wata sanarwa hukumar ta NCDC ke fitarwa duk mako tace, an samu karin mutum biyar da cutar ta harba a mako na 35

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta (NCDC) ta ce da yawan mutane da suka kamu da cutar kyandar biri ya kai 53.

Idan za a tuna a Rahoton mako na 34, hukumar ta ce mutum 48 ne suka kamu da cutar. Haka a mako na 33, adadin mutanen da suka kamu da cutar 40 ne.

Kusan makonni biyu da suka gabata Amurka ta ba Najeriya allurar rigakafin cutar ta kyandar biri, hakan ya sa ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta samu tallafin rigakafin.

“Allurar rigakain guda 10,000 za a raba su a jihohi biyar domin kare wadanda suke cikin hadarin kamuwar da cutar. Hakazalika a wannan mako Amurka ta ba Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo tallafin allurar rigakafi wacce it ace kasar da cutar ta fi Kamari.

“Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na aiki da sauran abokan hulda don ganin an kara fadada raba allurar rigakafin a sassan Afirka.” In Ji WHO.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *