Birnin Maiduguri dai yayi fama da ambaliyar ruwa mafi muni tun shekarar 1994, Wanda ruwa ya mamaye gidaje da dama, lamarin da ya sanya mazauna Borno cikin shirin ko ta kwana A lokacin
Alfijir Labarai ta rawaito Ambaliyar dai ta samo asali ne sakamakon ambaliya da madatsar ruwa ta Alau da ta cika a makon da ya gabata.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata mai taken “Alamar Ambaliyar Ruwa ga Mazauna Kogin Kogi,” Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, ya yi kira da a gaggauta ficewa daga yankunan da abin ya shafa, ya kuma bukaci mazauna yankin da su bi hanyoyin da aka kebe na ficewa domin kare lafiyarsu.
“Saboda yawan ruwan da ba a saba gani ba a bana, muna kira ga daukacin mazauna bakin kogi da su dauki matakin kare kansu da dukiyoyinsu cikin gaggawa.” Inji Tar. ” Dam din Alau ya keta wata tashar da a yanzu ke lalata gonaki, kuma ruwan ya nufi gabar kogi.”
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito, a karo na karshe da madatsar ruwan ta fuskanci irin wannan matsala a shekarar 1994, wanda ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye kusan rabin birnin Maiduguri.
Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) ta rawaito cewa bala’in ya sa daruruwan iyalai ke kwana a waje, inda da dama suka yi ta kokarin kwato duk wani abu da za su iya. Lamarin dai ya shafi daukacin unguwannin da ke gabar kogin, lamarin da ya sa akasarin mazauna yankin suka kasa shiga gidajensu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj