Ibtila’i! An Buɗe Katafaren Shagon Giya (Barasa) Na Farko A Saudiyya

FB IMG 1711032926613

An bude shagon shan barasa a kasar Saudiyya, irinsa na farko a tsawon shekarau 70.

Alfijir labarai ta rawaito an takaice shagunan ne ga jami’an huldar jakadancin kasashe da ke Saudiyyar.

Ana dai yi wa wannan mataki kallon wani kokari a kasar da ta haramta sayar da shan barasa tun shekarar 1952.

Tun dai a watan Janairu ne kasar ta sanar da cewa za ta bude shagunan sayar da barasa ga wasu kayyadaddun mutanen da ba Musulmi ba a birnin Riyadh.

Yanzu dai jama’a na saka ayar tambaya ga yunkurin kasar ta Saudiyya, inda suke neman sanin ko dai akwai yiwuwar kara fadada damar shan barasa a kasar fiye da takaice shi ga jami’an huldar jakadanci?

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *