Ibtila’i! An yi gargaɗi game da yiwuwar fuskantar ambaliya a jihohi 30 da kuma Abuja a Najeriya

FB IMG 1742320893164

Ministan Albarkatun Ruwa na Nijeriya, Joseph Utsev ya yi wannan gargaɗi ne ranar Alhamis yayin da yake gabatar da rahoto na shekarar 2025 kan Yiwuwar Aukuwar Ambaliyar Ruwa.

Alfijir labarai ta ruwaito ministan ya ce jihohin da ke fuskantar ambaliyar ruwa su ne Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da Babban Birnin Tarayya.

“Ƙauyuka 1,249 da ke ƙarƙashin ƙananan hukumomi 176 na jihohi 30 da Abuja suna fuskantar gagarumin hatsarin ambaliyar ruwa, sannan akwai ƙarin ƙauyuka 2,187 a ƙananan hukumomi 293 da ke fuskantar ambaliyar ruwa tsaka-tsaki,” in ji Minista Utsev.

Ya ƙara da cewa jihohin da ke fuskantar gagarumar ambaliyar ruwa sun haɗa da Abia, Benue, Lagos, Bayelsa, Rivers, da Jigawa.

A cewarsa, jihohin da ke gaɓar teku za su fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon ƙaruwar ruwan sama da tasirin sauyin yanayi.

Ministan ya ce an fitar da wannan gargaɗi cewa tare da yin bayani dalla-dalla game da wuraren da lamarin zai shafa domin kauce wa samun gagarumar asarar rayuka da ta kayayyaki.

Joseph Utsev ya ce gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwa da sauran ɓangarori suna ɗaukar matakan rigakafi tare da ƙoƙarin ganin an kauce wa mummunan tasiri na ambaliyar ruwan.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *