Kotu Ta Baiwa Gwamantin Kano Umarnin ta Biya Alasan Doguwa Diyyar Miliyan 25

FB IMG 1718100219352

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana Hon. Alhassan Ado Doguwa, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, ba shi da laifi kan zargin kisan kai da gwamnatin jihar Kano take Zargin sa da aikatawa

Alfijir labarai ta ruwaito Alkali D.U. Okorowo ya wanke Doguwa daga tuhumar kisan kai. Kotun ta kuma umarci Gwamnatin jihar Kano da ta biya Ado Doguwa diyyar Naira Miliyan 25.

Doguwa, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Kan Man Fetur, kuma mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a Jihar Kano, Gwamnatin NNPP ta zarge shi da laifin kisan kai.

‘Yan sanda sun kama Doguwa a Kano tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa laifin kisan kai. Daga baya wata kotu ta sake shi bayan da ya nemi a sake duba binciken da ‘yan sanda suka yi wanda ya kai ga kama shi, aka Gurfanar dashi a Gaban kuliya, Tare da tsare shi.

Gwamnatin APC da ta gabata a jihar ta yi watsi da binciken tare da wanke shi. Sai dai kuma gwamnatin New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta sake bude shari’ar, inda ta zargi Doguwa da kashe sama da mutane 15, galibi ‘yan jam’iyyar NNPP.

A martanin da ya mayar, Doguwa ya kai karar Babban Lauyan Tarayya, Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Gwamnan Jihar Kano, da Babban Lauyan Jihar Kano bisa zargin tauye masa hakkinsa na mutunci, ’yanci, da kuma ’yancin tafiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *