Ibtila’i! Gobara ta Tashi A Wani Otel Cikin Dare Ana Cikin Shakatawa A Kano

FB IMG 1709891079107

Wasu da ake zargin masu yawon ta zubar ne sun tsallake rijiya da baya, bayan gobara ta tashi a otel din mairabo da suke shakatawa a unguwar Sabon gari dake karamar hukumar Fagge a jihar kano

Alfijir labarai ta rawaito rahotanni sun tabbatar da cewa an garzaya da wasu mutane hudu zuwa Asibiti a daren jiya bayan samun raunika, a sakamakon fadowa ta taga daga kan benen otel din mai hawa uku dake kan titin Aitken a yankin sabon gari .

Majiyar mu ta bayyana mana cewar mutanen hudu sun hada da maza biyu da mata biyu, wanda suke tsaka da shakatawa a cikin dakunan dake otal din, a lokacin da gobarar ta tashi, lamarin da ya tilasta masu fadowa daga kan tagogin otal din zuwa kasa, kamar yadda aka gani cikin wani faifan bidiyo.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki wanda yasa daya daga cikin na’urorin sanya wurin ya kama da wuta.

Jami’an yan sanda da kuma jami’an kashe gobara sun yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru domin kashe wutar, kuma zuwa yanzu dai babu rahoton samun asarar rai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *