Kotu Ta Gargadi Gwamnan Kano Da Majalisar Dokokin Jihar kan Kananan Hukumomi

FB IMG 1695680993148

Babban kotun tarayya dake zamanta a jihar kano karkashin jagorancin mai shari’a M A Liman ya umarci gwamnatin jihar da majalisar dokokin da su dakatar da shirinsu na nada Kantomomi a kananan hukumomi jihar 44.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata takardar Umarni da kotun ta fitar mai dauke da umarni kusan 4, wacce take dauke da kwanan watan 7 ga watan maris, 2024.

Cikin kunshin Karar da wani Haruna Abbas Babangida ya shigar, alƙalin kotun ya kuma umarci babban akanta na kasa da babban lauyan kasar nan kuma ministan Shari’a da kada su sake gwamnatin tarayya ta sakawa kananan hukumomin jihar kano kudaden wata-wata muddin aka nada Kantomomi har sai an kammala sauraren Shari’ar.

Kotun dai ta umarci dukkanin bangarorin da kowa ya tsaya a Inda yake har sai kotun ta gama sauraron Shari’ar.

Mai Karar ya bukaci kotun da ta dakatar da gwamnati da majalisar dokokin jihar kano daga nada Kantomomi, sannan kuma kotun ta baiwa babban akanta na kasa Umarnin kada su turawa Kantomomi kudaden kananan hukumomi saboda ba zababbu bane, nada Kantomomin ya sabawa tsarin dimokaradiyya.

Idan za’a iya tunawa ranar Litinin data gabata gwamnan jihar kano ya turawa majalisar dokokin jihar wasikar neman Amince masa ya nada Kantomomi a kananan hukumomi 44 sakamakon karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin a ranar 12 ga watan da ya gabata.

A jiya dai majalisar ta bada sanarwar ta kammala aikin tantance sunayen shugabannin riko na kananan hukumomin da gwamnan jihar kano ya tura musu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *