Wata gobara da ta tashi a yau Laraba, ta yi sanadin mutuwar wasu ‘yan uwa uku na Dakta Yusuf Kofar Mata, kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano.
Alfijir labarai ta ruwaito Dr. Kofar Mata ya bayyana wannan mummunan labarin ne da safiyar Laraba ta shafin sa na Facebook.
A cewar sanarwar, ‘yarsa Maimuna (Islam) da babbar yayarsa Hajiya Khadija da matar dan uwansa Hajiya Juwairiyya sun rasu sakamakon gobarar da ta tashi.
A nasa bayanin, Dakta Kofar Mata ya bayyana matukar bakin cikinsa, inda ya ce, ‘Ina jimamin rashin ‘yata Maimuna (Islam), babbar kanwata Hajiya Khadija, da matar dan uwana, Juwairiyya, wadanda suka mutu a gobara. Za a yi Sallar Jana’izar su da karfe 11:00 na safe a kofar Mata da ke cikin birnin Kano.’
Hukumomi da na binciken musabbabin tashin gobarar yayin da ‘yan uwa da abokan arziki da abokan aikinsu ke mika ta’aziyya ga Dakta Kofar Mata da iyalansa a wannan sa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj