Labari Mai Dadi! Mahaifiyar Rarara Ta Kubuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga

FB IMG 1721202405306

Mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar nan na Arewacin Nijeriya, Dauda Kahutu Rarara ta kubuta daga hannun ‘yan bindigar da suka sace ta.

Alfijir labarai ta ruwaito idan za ku iya tunawa an sace mahaifiyar mawakin, Hauwa’u Adamu a ranar 28 ga watan Yuni, 2024 a kauyen Kahutu da ke karamar hukumar Danja a Jihar Katsina.

Sai dai bayan sace tsohuwar mai shekaru 75 a duniya, jami’an ‘yansanda a jihar suka baza koma, inda suka cafke mutum biyu da suke zargi da hannu a sace ta.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce an sace mahaifiyar mawakin da misalin karfe 1:30 na dare.

Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da kubutar mahaifiyar mawakin, amma babu cikakken bayani ko an biya kudin fansa kafin sakinta.

Leadership Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *