Ibtila’i! Wata Mota Kirar Tirela Ta Kashe Mutum 14 A Jigawa Wadanda Suka Taho Daga Kano

Screenshot 20240717 171347 Chrome

Akalla mutane 14 ne suka mutu huɗu sun jikkata a wani hatsarin mota da ya auku inda wata tirela da wata mota kirar Toyota Hiace Bus suka yi arangana a kasuwar Kanya ta jihar Jigawa.

Alfijir labarai ta ruwaito kakakin Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam, ya shaida wa WikkiTimes cewa, hadarin ya faru ne bayan da wata mota kirar Toyota Hiace ta yi taho-mu-gama a kasuwar Kanya da motar Tirela da yammacin ranar Talata.

Rahotanni sun ce Tirelar ta fito ne daga kasuwar Kanya amma ta tsaya a wani shingen bincike na Immigration, sai wata mota kirar Toyota Hiace da ke cikin sauri ta kutso kai inda tayi cikin tirelar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji 14 da ke cikin motar.

Shaidar gani da ido mai suna Adam ya ce nan take mutane 14 suka mutu yayin da wasu hudu ke kwance a asibiti.

A cewarsa, direban Hiace ya fito ne daga Kano inda ya kauce hanya a wani mataki na neman kaucewa shingen binciken.

“A yau Talata, 16 ga Yuli, 2024, bayanai daga rundunar ƴan sandan sun nuna cewa an samu mummunan hatsarin mota inda wata motar Tirela kirar Daf ta markaɗe wata karamar mota ”.

”Da isar motar wurin shine sai wata motar, Toyota Hiace mai lamba Shima XA 381 GAS wacce ta tahowa daga Kano zuwa Kasuwar Kanya dauke da kaya da yawa kuma cikin sauri”.

“Lokacin da jami’an shige-da-ficen suka tsayar da shi, direban ya ki tsayawa sai ya yi yunkurin zagaye shingen ta hanyar bi ta dayan hanyar. Sakamakon haka, ya yi karo da babbar motar Daf,” in ji Adam.

Ya ƙara da cewa an tabbatar da mutuwar fasinjojin tare da kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Kanya Babba Cottage.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *