Ibtila’i: Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ya kashe kansa a Oyo.

FB IMG 1703222676383

Har zuwa lokacin mutuwarsa, DCP ya yi aiki a FCID Annex Alagbon kusa, dake Ikoyi Legas.

Alfijir labarai ta rawaito wani jimami ya afku yayin da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar oyo, Gbolahan Olugbemi ya kashe kansa da kansa a jihar Oyo.

DCP Olugbemi, wanda ke aiki a sashin leken asiri da binciken manyan laifuka shiyyar Alagbon, Legas, ya rasu ne a gidansa da ke Ògbómọ̀ṣọ́, jihar Oyo, inda ya je hutun Ista.

Ya kasance mai taimaka wa marigayi tsohon gwamnan jihar, Adebayo Alao-Akala, a tsawon watanni 11 da ya yi yana gwamna a shekara ta 2006.

Wata majiya ta ce, DCP Gbolahan wanda ya saba ziyartar garinsu a lokacin bukukuwan Ista, ya shaida wa mataimakansa a karshen mako da su je garuruwansu daban-daban domin yin bikin tare da ‘yan uwansu.

Majiyar ta ce, “Eh, ya kashe kansa. An tsinci gawarsa rataye a gidansa jiya ranar (Litinin). Shi kadai ne a gidan, kuma yakan dawo gida don bikin Ista.

“A wannan karon, ya gaya wa mataimakansa su je su he su yi biki tare da danginsu a gidajensu daban-daban. Allah ne kadai ya san abin da zai iya sa shi kashe kansa.”

Har zuwa lokacin mutuwarsa, DCP ya yi aiki a FCID Annex Alagbon kusa, dake Ikoyi Legas.

Amma rundunar ‘yan sanda ta bakin mai magana da yawun FCID, ASP Aminat Mayegun ta ce za su gudanar da bincike kan mutuwarsa inda ta kara da cewa tsohon mataimakin marigayi DIG Israel Ajao da marigayi CP Young Arebame sun ce basusan dalilan kashe kan nasa ba.

Rundunar ‘yan sandan ta ce za ta binciki wanda ya fara ganin gawarsa, inda ya fito da kuma wanda yake tare da shi a lokacin da ya shiga dakinsa ciki har da wanda ke da wayoyinsa guda biyu har zuwa lokacin da ya mutu.

Olugbemi, wanda ya samu horo kan ayyukan ta’addanci da kuma yaki da ta’addanci a ayyuka, ya samu lambobin yabo da dama a Najeriya da kuma kasashen waje, kuma an yi masa shagulgula a kafafen yada labarai bisa ayyukan alheri da ya yi a tsawon rayuwarsa.

Ya yi karatun digiri a Jami’ar Legas da Jami’ar Olabisi Onabanjo kafin cikar sa’in na sa.

IMG 20240402 WA0451
Late

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *