Hukumar kiyaye hadurra ta Kasa (FRSC) ta ce mutum tara sun rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hadarin mota da ya faru a kan titin Malumfashi-Kafur a Jihar Katsina.
Shugaban sashen FRSC na jihar, Aliyu Ma’aji, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi inda ya ce hadarin ya shafi wata motar Hummer dauke da fasinjoji 20.
Ma’aji ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa gudu fiye da kima da direban motar ya yi ne ya haddasa hadarin.
Shugaban hukumar ya yi kira ga direbobi da su guji gudu fiye da kima, daukar fasinjoji fiye da yadda doka ta tanada da kuma tukin ganganci, musamman a lokutan bukukuwa.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD