Ibtila’i! Sanadin Cin Faten Wake Mai Guba Ya Hallaka Daliban Makaranta 3

Wake

Daga Aminu Bala Madobi

Wata balahira da ta wakana ga wasu ’ya’yan wani mai makaranta su uku, wanda nan take suka rasu bayan da ake zargin sun ci guba a waken da aka sarrafa alala a jihar Enugu.

Alfijir labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a unguwar Agu-Uwani, Akwuke, dake tsakkiyar karamar hukumar Enugu ta Kudu a jihar.

Wadanda lamarin ya shafa ‘ya’yan Mista Callistus Egbo ne, mai makarantar firamare da sakandare ta Elohim, Agu-Uwani, wanda ya fito daga Nenwe, karamar hukumar Aninri ta Enugu.

Rahotanni sun ce iyalan sun ci waken ne da yammacin ranar Talata kuma ba da dadewa ba suka kamu da rashin lafiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar yaro daya a yammacin ranar, yayin da sauran yaran biyu suka rasu a ranar Laraba.

Mahaifin yaran da suka rasu, Callistus Egbo, na fama da matsananciyar rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Enugu, kamar yadda wani faifan bidiyo da ke ta yawo a karshen mako.

Lamari mai ratsa zuciya ya jefa al’umma cikin fargaba, tare da nuna damuwa game da lafiyar abinci da muhimmancin sarrafa abinci da kuma duba shi yadda ya kamata kafin a ci.

Wata majiya da ke kusa da wurin da lamarin ya faru ta ce sakamakon wannan lamari, yanzu haka mutane da dama a yankin na kauracewa abincin wake irin su kosai da kuma alala wato Moi Moi.

“Hakika babban abin jimami ne da lamarin ya afkawa ‘yan uwa. Tun bayan faruwar lamarin kwanaki uku ko hudu da suka gabata, babu wanda ke cin wake a yankinmu, hatta kosai da Moi Moi.

Kaje Kasuwar Garriki da shagunan kan tituna ka duba ko akwai mai sayar da Moi Moi ko kosai ka gani?

A halin da ake ciki dai hukumomi a jihar sun yi shiru ba suce ko da uffan ba kan lamarin domin kuwa rundunar ‘yan sanda ko gwamnatin jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *