Wata Sabuwar! Kimanin Malamai 30 Ne Suka Yi Murabus a Jami’ar Bauchi.

Gidan Zoo

Daga Aminu Bala Madobi

Kimanin sama da malaman jam’iar Sa’adu Zungur (SAZU) 30 ne suka yi murabus sakamakon tabarbarewar yanayin aiki da kuma rashin isassun abubuwan jin dadin rayuwa.

Alfijir labarai ta rawaito cikin wani rahoto bayan wata ganawa da manema labarai, inda jami’an kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), shiyyar Bauchi suka bayyana damuwarsu kan yadda alamuran ke garawa.

Kungiyar tace babu wani ingantaccen tsari na kammala aiki balle an sami saukin rayuwa wanda hakan ke tilasta wa da yawa manyan malaman mu ke neman wata dama a wasu wurare, in ji kodinetan kungiyar ASUU na shiyyar Bauchi, Namo Timothy.

“SAZU ba ta da tsarin fansho ko fa’idar mutuwa kamar yadda aka samu a cikin tsarin ma’aikatan gwamnati a kasar.”

Ya ce ba tare da tsarin fansho ko na mutuwa ba, mambobinmu suna samun damuwa matuka, hankalin su bai kwantawa game da sanin makomarsu.

Kungiyar ta kuma soki hukumar gudanarwar jamiar da gaza biyan sama da naira miliyan 650 na kudaden da aka tara, da suka hada da alawus alawus na karatu da kuma karramawa ga zakakuran malamai a cikin gida.

“Jami’ar ta yi ikirarin cewa babu wasu kudade da za ta biya mambobinmu, amma duk da haka tana ci gaba da dora wa daliban kudade,” in ji Timothy.

Dangane da wannan kalubalen, ASUU shiyyar bauchi tana kira ga gwamnatin jihar Bauchi da masu ruwa da tsaki da su gaggauta magance jin dadin ma’aikatan da suka hada da samar da cikakken tsarin fita daga aiki da kuma aiwatar da kudaden alawus-alawus da ba su wuce ba.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kafa dokar ta-baci a jami’ar, don ta hakane za a magance duk wasu batutuwan da ke haifar da cece-kuce domin tabbatar da makomar ma’aikatan ilimi.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *