Ibtila’i! Wani Katafaran Gini Ya Rufta Kan Wasu Mutane A Abuja

Screenshot 20240713 151654 Facebook

Lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan da ginin wata makaranta ya rufta kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa a Jos.

Alfijir labarai ta ruwaito ana fargabar cewa a halin yanzu mutane da dama sun maƙale a ƙarƙashin baraguzan wani ginin bene mai hawa biyu da ya rufta a unguwar Kubwa da ke Abuja a safiyar ranar Asabar.

Kawo yanzu babu wasu cikakkun bayanai dangane da faruwar lamarin, amma wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun ce ginin da abin ya shafa ya rufta ne da misalin ƙarfe 7 na safe.

Bayanai ce masu bayar da agajin gaggawa na kan hanyarsu ta zuwa wurin da lamarin ya faru a yayin da hotuna da bidiyo suka nuna yadda jama’a ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya shafa.

Wannan lamari dai ya faru ne sa’o’i 24 bayan da ginin wata makaranta ya rufta kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa a Jos, babban birnin Filato.

Aƙalla mutane 22 ne suka mutu sannan 132 suka samu raunuka kamar yadda wata sanarwar da gwamnatin Jihar Filato ta fitar a daren Juma’a.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *