Ibtila’i: Wasu Dalibai Mata Biyu Sun Mutu Sakamakon Turmutsutsun Rabon Abinci

IMG 20240323 WA0004

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnan jihar Nasarawa Engr. Abdullahi Sule ya bayyana kaduwa da labarin turmutsutsu da ya wakana a Jami’ar Jihar Nasarawa dake Keffi da safiyar Juma’a 22/03/2024.

Alfijir labarai ta rawaito a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Ibrahim Musa Addra ya fitar a garin Lafia, gwamnan ya bayyana kaduwarsa kan mutuwar dalibai mata biyu sakamakon lamarin.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da wasu da ake zargin barayi ne da wasu batagarin daliban makarantar suka kutsa harabar gurin taron makarantar inda suka kwashe shinkafar da aka ajiye a wurin da ake shirin rabawa dalibai.

Sakamakon turmutsitsin ne ya sa biyu daga cikin dalibai mata suka gamu da ajalinsu, yayin da goma sha bakwai daga cikinsu suka samu raunuka daban-daban kuma nan take aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Sai dai wakilinmu ya rawaito cewa, daga baya ‘yan sandan sun bi daliban da suka yi sa’ar tserewa da wasu buhunan shinkafar zuwa dakunansu, inda suka kwaso buhunan shinkafar, lamarin da bai yi wa daliban da suka yi awon gaba da kayan agajin da dadi ba.

Engr. Sule dai ya fito da shirin da jama’a suka yaba da shi na raba shinkafa da tsabar kudi Naira 5000 ga kowanne dalibi a dukkan manyan makarantun jihar.

Irin wannan rabon ya samu gagarumar nasara kuma an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali a Jami’ar Tarayya da ke Lafia, da Isa Mustapha Agwai Polytechnic, Lafiya, Kwalejin Aikin Noma, Kimiyya da Fasaha, Lafia, Makarantar koyon aikin jinya da Kwalejin Ilimi ta Akwanga.

Sauran sun hada da makarantar fasaha ta tarayya, Kwalejin Fasahar Lafiya ta Keffi.

Gwamna Sule ya nuna matukar takaici bisa rasuwar daliban makarantar biyu a cikin wannan turmutsutsu.

Gwamnan ya ce “Ina rokon Allah ya ji kan su wanda sukaji raunuka ya ba su lafiya. Rayuwar wadannan dalibai mata sakamakon turereniyar kwasar kayan abinci.

Tuni dai Gwamnan ya umarci mahukuntan Jami’ar Jihar dake Keffi da kuma hukumomin tsaro da su fara gudanar da binciken gaggawa kan lamarin da nufin bankado masu hannu a ciki.

Anasa bangare mataimakin gwamnan jihar Dr. Emmanuel Agbadu Akabe ya ziyarci jami’ar domin gano gaskiyar lamarin. Ya kuma ziyarci wadanda suka samu raunuka.

Gwamnan ya bukaci da a kwantar da hankula yayin da ya jaddada cewa gwamnati karkashin jagorancin sa za ta yi kasa a gwiwa ba domin hukunta masu hannu cikin lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *