ICPC ta tsare tsohon Darakta-Janar na NIMASA, Bashir Jamoh

FB IMG 1770225002218

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) ta tsare tsohon Darakta-Janar na Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Nijeriya (NIMASA), Bashir Jamoh.

Majiyoyi sun bayyana a daily Trust cewa an kama Jamoh ne bayan da ya kasa amsa gayyatar da ICPC ta yi masa sau da dama, biyo bayan koke-koken da aka shigar a kansa.

Ana zargin tsohon shugaban NIMASA da saba ka’idar aiki  ta hanyar ba wa kansa fa’ida ba bisa ka’ida  na a wasu hanyoyin saye da samar da kaya.

Kakakin ICPC, John Odey, ya tabbatar da kama Jamoh, amma ya ce hukumar ba za ta bayyana cikakken bayani kan zargin da ake masa ba a halin yanzu.

Jamoh ya jagoranci NIMASA daga shekarar 2020 zuwa 2023.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *