Idan Na Ce Laifin Tinubu Ne Matsalar Tattalin Arzikin Ƙasa Ban Masa Adalci Ba — Sarki Sanusi

FB IMG 1707738314590

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi ll ya bayyana cewa bai yi adalci ba ya idan ya soki Shugaba Bola Tinubu kan matsalar tattalin arzikin kasar.

Alfijir labarai ta rawaito Muhammadu Sanusi, ya zargi gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari a kan munanan manufofinta na tattalin arziki.

Ya ce gwamnatin Buhari ta yi watsi da shawararsa kan yadda za ta fitar da Najeriya daga matsalolin tattalin arziki.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya yi magana ne yayin wani taron addini da aka gudanar a ranar Lahadi.

Ya ce da gangan yan Najeriya da ke sa ran zai yi magana kan matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi ne ke son ya soki Tinubu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *