Yadda Ta Kasance A Ganawar Shugaba Tinubu Da Kungiyar Tijjaniyya Ta Duniya

FB IMG 1707678615279

shugaban ya bayyana tsare-tsaren inganta noma ta hanyoyi daban-daban, da suka hada da fadada filayen noma, samar da rance mai sauki ga manoma, da kuma zuba jari mai yawa a bangaren samar da noma.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na kawo sauyi a harkar noma domin ganin Najeriya ta dogara da kanta wajen samar da abinci da kuma fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen waje.

Da yake jawabi a lokacin da ya karbi tawagar kungiyar Tijjaniyya ta Duniya, karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Lahadi, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta goyi bayan tsare-tsare da kuma kokarin bayar da sauki da taimako ga alhazai.

Ya kuma jaddada muhimmancin ayyukan ibada wajen gina kasa, inda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafawa ayyukan addini.

Ya bayyana bukatar yin hadin gwiwa tsakanin shugabannin siyasa da na jama a, don ciyar da muradun al’umma da inganta hadin kai a tsakanin jama’a.

A bangaren noma kuwa, shugaban ya bayyana tsare-tsaren inganta noma ta hanyoyi daban-daban, da suka hada da fadada filayen noma, samar da rance mai sauki ga manoma, da kuma zuba jari mai yawa a bangaren samar da noma.

“Mun sadaukar da kai wajen samar wa asibitoci kayan aiki na zamani, samar da kwararrun masana kiwon lafiya horo, da kuma tabbatar da jin dadin jama’a ga kowane dan kasa, gami da cikakken tsarin inshorar lafiya.

“Najeriya za ta zama kasa mai fitar da abinci, muna kawo dubunnan taraktoci, za a habaka noman abinci ta yadda za a yi amfani da karfin tuwo, dole ne mu zama masu albarka a matsayinmu na al’umma. Wannan ita ce Sunnah da ka’idojin da na taso na fahimta.” In Ji shi.

FB IMG 1707678625533
📸 Presidency

Shugaba Tinubu ya godewa kungiyar Tijjaniyya ta Duniya bisa goyon baya da addu’o’i da suke yi, inda ya jaddada muhimmancin kokarin hadin gwiwa wajen gina Najeriya mai inganci.

Sheikh Mahe Niass, Khalifan Tijjaniyya, wanda yake magana a madadin tawagar, ya yabawa shugaba Tinubu bisa jajircewarsa na ganin Najeriya ta samu zaman lafiya, ci gaba, da kwanciyar hankali.

Ya kuma bayyana amincewa da shugabancin shugaban kasar tare da mika goyon baya da addu’o’in ‘yan kungiyar Tijjaniyya ta Duniya ga shugaban Najeriya.

A yayin ziyarar tasu, tawagar ta gabatar da addu’o’in ci gaban kasar nan, da hadin kai da kuma ci gaba, tare da rokon Allah Madaukakin Sarki Ya kara wa Shugaba Tinubu hikima, karfin gwiwa, da nasara.

FB IMG 1707678605262
📸 Presidency

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *