IGP ya nada sabbin jami’an hulda da jama’a na ‘yan sanda

FB IMG 1693991306327

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya amince da sanya jami’an hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPROs) zuwa wasu kwamitoci da tsare-tsare a rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Alfijir Labarai ta rawaito an bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun ACP Olumuyiwa Adejobi, jami’in hulda da jama’a na rundunar [FPRO]

Ya ce wadannan nade-naden na da matukar amfani wajen inganta sadarwa, gaskiya, da kuma hada kan al’umma a yankunan da abin ya shafa.

Sabbin PPRO da aka nada sun hada da

DSP Chukwukadibia O. Omojola zuwa PPRO Railway Command;

ASP Mansir Hassanto zuwa PPRO Jihar Kaduna;

ASP Nahum Daso Kenneth zuwa PPRO Jihar Borno;

ASP Mayegun Aminat Oluwakemi zuwa PPRO Force Force Investigation Annex, Legas.

Wadannan jami’an, a cewar sanarwar, an zabo su ne a tsanake, bisa la’akari da kwarewarsu ta aiki, dabarun sadarwa, da kuma jajircewarsu wajen samar da kyakkyawar alaka tsakanin ‘yan sanda da jama’a.

“Za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da amana tsakanin rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran al’umma.”

Sanarwar ta kara da cewa, Sufeto Janar na ‘yan sandan yana taya sabbin PPROs da aka nada murna kan sabbin mukaman tare da bayyana kwarin guiwarsu na iya gudanar da ayyukansu tare da sadaukarwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *