Inda Ba Kasa: Almajirai da ƴan jari-bola sun maka Ministan Abuja, Wike a kotu

FB IMG 1736943864937

Almajirai da ƴan jari-bola mazauna babban birnin tarayya Abuja da suka hada har da kananan ƴan kasuwa, da sauransu, sun shigar da kara akan ministan Abuja, Nyesom Wike, inda su ka bukaci ya biya su diyyar Naira miliyan 500 bisa zargin sa da tauye ƴancin su na yan ƙasa.

Wani lauya mai suna Abba Hikima ne ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1749/3024 a gaban mai shari’a James Omotosho na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a madadin rukunin mutanen.

Hikima, wanda aka ambata a matsayin mai shigar da ƙara a cikin takardar ƙarar da aka fitar a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024, amma aka shigar a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2024, ya ce ya kai kara ne domin al’umma domin kare ƴan kasa masu rauni a Najeriya.

Masu ƙarar, kamar yadda Daily Trust ta rawaito, na ya haɗa da Wike, Sufeto-Janar (IG) na ‘yan sanda; Darakta-Janar, Sashen Sabis na Jiha (DSS) da Hukumar Tsaron farar hula  (NSCDC) a matsayin waɗanda ake kara na 1 zuwa 4.

Lauyan ya kuma hada da Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Gwamnatin Tarayyar Najeriya a matsayin waɗanda ake kara na 5 zuwa 6.

Ya kuma nemi a biya Naira miliyan 500 a matsayin diyya saboda take hakkin ƴan kasa da abin ya shafa.

Ya yi roko ga kotun da ta bayyana cewa “kame ba bisa ka’ida ba, tsarewa ba tare da tuhuma ba, cin zarafi da karbar kuɗaɗe a wajen wadanda ba su da matsuguni, ‘yan banga, kananan ‘yan kasuwa, mabarata da sauran ‘yan Najeriya marasa galihu mazauna babban birnin tarayya Abuja, ya zama cin zarafi da take ƴancin su na yan kasa.

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *