INEC Ta Saka Ranar Kammala Zaɓukan Da Basu Kammala Ba


Alfijr ta rawaito INEC ta sanya ranar Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranakun da za ta kammala zabukan da ba a karasa ba a kasar.

Rotimi Lawrence Oyekanmi, babban sakataren yada labarai na shugaban INEC ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin.

Baya ga wannan, a wani sako da hukumar ta kuma wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta yanke shawarar ne bayan wata ganawa da ta yi da jami’an hukumar a wannan Litinin din.

Hukumar ta saka ranar Asabar 15 ga watan Afrilun ne, za a karasa zabukan gwamnoni da na ’yan majalisun dokokin da ba a karasa ba, sakamakon wasu matsaloli.

Idan zaku tuna, INEC dai ta ayyana zabukan gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *