Innalillahi! Kamfanin NNPCL Ya Ƙara Farashin Litar Mai A Najeriya

FB IMG 1724920196312

Daga Aminu Bala Madobi

Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya sanar da sabon farashin litar man fetir a fadin kasar da sanyin Safiyar Talata

Alfijir Labarai ta rawaito a wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.

Tuni dai wasu gidajen maI a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a ranar ta Talata.

Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya ke hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashi ne.

Da ma dai kafin sanar da sabon farashin na ranar Talata, dogayen layukan ababan hawa sun mamaye gidajen mai a biranen Abuja da Legas.

Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa.

NNPC
NNPC

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *