Allah yayi wa Shahararren ɗan jaridar nan Ahmad Isah Koko rasuwa.
Malam Ahmad Koko, ya rasu ne a yau Alhamis bayan fama da jiyya, yayin da ake sa ran gudanar da jana’izarsa a gobe Juma’a.
Kafin rasuwarsa dai ya shahara wajen karanta littattafan Hausa a gidajen rediyo a ciki da wajen Najeriya, musamman Rai Dangin Goro
Haka kuma karatun nasa yana matuƙar jan hankalin Mata da Matasa, duba da yadda yake sarrafa muryarsa domin yin muryoyin jinsin Mutane a mataki daban-daban.
Bugu da ƙari ya kasance tsohon ma’aikacin Rediyo Najeriya, kuma tsohon shugaban Sashen Hausa na Bond FM.
Da fatan Allah ya jiƙansa ya rahamshe, ya kuma bawa dukkan ‘yan uwa da abokan arziƙi haƙurin wannan rashi.
GTR Hausa
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj