Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Zuru ta Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Sani Sami (Gomo II), rasuwa bayan gajeriyar jinya.
Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin Masarautu na jihar Kebbi, Garba Umar Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Safiyar yau Lahadi, inda ya ce Sarkin me kimanin shekaru 81 a duniya, ya rasu ne a daren jiya Asabar a wani asibiti da ke birnin Landan.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan Marigayin, Masarautar Zuru da kuma Al’ummar jihar Kebbi gaba daya, tare da fatan Allah ya jikansa ya rahamshe shi.
Sanarwar ta ce za a sanar da lokacin Jana’izar Marigayin a nan gaba kadan. Ya kuma rasu ya bar Mata Hudu da kuma Yara Bakwai.
An haifi Marigayin a ranar 24 ga watan Oktoba na shekarar 1943, inda ya shiga aikin Soja a ranar 10 ga watan Disambar 1962, bayan ya karbi horo a kwalejin Mons Officer Cadet da ke Aldershot ta kasar Birtaniya, tare da abokan horonsa ciki har da tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Marigayin ya riƙe manyan mukamai masu muhimmanci a zamanin Janar Murtala Ramat Mohammed, inda ya shugabanci Brigade of Guards a Legas. Daga bisani, bayan juyin mulkin 1983 da ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki, aka naɗa shi gwamnan soja na Jihar Bauchi, daga watan Disamba 1983 zuwa Agusta 1985.
Bayan ya yi ritaya daga aikin Soja ne aka naɗa shi Sarkin Zuru, inda ya shahara da kishin ci gaban al’umma, sauƙin kai, da jajircewa wajen kare al’adun gargajiya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t