A yau ne Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Ibrahim Abdullahi Waiya ya jagoranci rantsar da sabbin Mambobin kungiyar kwararrun masu hulda jama’a ta ƙasa NIPR a dakin taro na Tahir Hotel.
A yayin tattauna da manema labarai Kwamishinan yace wannan shine karo na farko da gwamnatin mai girma Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ya ɗauki nauyin Mutun 71, domin zama Mambobin wannan kungiyar da take saka ido akan yadda mutane masu hulda da jama’a suke gudanar da aikinsu, kuma aka rantsar da su a yau.
Waiya ya kara da cewar wannan shine karo na farko nan gaba kadan za a kuma ɗaukar mutum 50, ko sama domin sake horar da su.
Kwamishinan ya kuma ja hankalin wadannan suka samu wannan horon wajen zama da jakadun kirki, ya kuma ce a baya daidaikune ne suke samun damar yin wannan rigista saboda yawan kuɗin amma yanzu gashi gwamna ya jikan ku.
Farfesa Sule Ya,u yaja hankalin sababbin lambobin wajen zama jakadun kwarai da kuma yin aikinsu yadda ya kamata, sannan kuma yace shiga almarun kungiyar shine zai taimaka musu wajen sanin abinda ya kamata ba wai don sun ƙarbi saidarsu su koma gefe ba.
A karshe ya yabawa gwamnatin Kano da Kwamishinan yaɗa labarai da ayyukan cikin gida wajen jajircewa domin bada wannan damar ta farko a jihar Kano.











Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t