Jami’ar Bayero ta amince da korar dalibai 171

IMG 225430 23326 1774302882665

Bayero University (BUK) ta amince da korar dalibai 171 bisa laifin gabatar da takardun shaidar shiga jami’a na bogi.

An cimma wannan matsaya ne a taron majalisar dattawan jami’ar karo na 433, bayan rahoton da Kwamitin Majalisar kan Matsalolin Takardun Shiga Jami’a ya gabatar.

A cewar wata sanarwa da aka wallafa a cikin mujallar mako-mako ta jami’ar, an gano cewa ɗaliban da abin ya shafa sun gabatar da takardun bogi yayin neman gurbin karatu, wanda ya saɓa da dokokin jami’ar.

BUK ta ƙara da cewa ɗaliban sun fito daga sassa da matakai daban-daban, inda ta jaddada cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin tsaftace bayanan karatu da kuma tabbatar da ingancin tsarin ilimi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *