Jam’iyyar APC Kano Ta Magantu Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli Da Ya Gabata

FB IMG 1693497487701

Jam’iyyar APC a Kano sun ce sun rungumi ƙaddara game da hukuncin kotunƙolin Najeriya da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Alfijir labarai ta rawaito Sakataren jam’iyyar na jiha Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida wa BBC cewa sun karɓi ƙaddara, suna kuma fatan hakan ya zame musu alkairi.

Ya ce kuma suna kyautata wa Allah zato cewa tabbas hakan zai zama alkairi a gare su.

”A yanzu muna cikin alhini, kuma bai kamata mu ɗauki mataki a lokacin alhini ba, amma idan ƙura ta lafa, za mu zo mu zauna, mu shirya domin tunkarar zaɓen 2027”.

Tun da farko dai jam’iyyar ce ta yi nasara a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara, kafin yau kotun ƙoli ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan farkon.

”Allah ya sa hakan ne ya fi alkari, kuma muna bai wa ‘yan jam’iyar mu na APC da sauran al’ummar jihar kano hakuri, tare da kiran a zauna lafiya”, in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *