Alfijr ta rawaito auren nan da aka jima ana tsimayen sa, wato na jarumar Kannywood, Ruƙayya Umar Santa (Dawayya) da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Isma’il Na’abba (Afakallah) ya matso kusa
Alfijr Labarai
Binciken alfijr ya tabbatar da tsantsar soyayya tsakanin Dawayya da Afakallah duba da yadda ake takun Boye.
“Soyayya ce da aka daɗe ana yin ta a ƙarƙashin ƙasa, ba tare da sun bayyana wa duniya ta sani ba, sai a yanzu da aski ya zo gaban goshi ne ya sa ita Ruƙayya Dawayya ta fara ɗora hoton Afakallah a ‘status’ ɗin ta na WhatsApp da TikTok da kuma Instagram tare da yin wasu bayanai masu nuna alamar akwai soyayya mai ƙarfin gaske a tsakanin su.”
Majiyar ta ƙara da cewa: “Akwai maganar auren, kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci za a iya yin sa.
“Ana cewa ba wani taro za a yi ba, za dai a ɗaura aure ne kawai amarya ta tare, amma dai mu mun dage a kan lallai sai an yi dina.
Dawayya ba ƙaramar jaruma ba ce, kuma shi oga kowa dai ya san matsayin sa da muƙamin sa a gwamnati da ma siyasa, don haka, za mu yi biki sosai.
Alfijr Labarai
“Da zarar sun kammala shirin da su ke yi, za a ji sanarwar ɗaurin auren. Ba wani abu ba ne da za mu ɓoye.”
A saƙon da ta wallafa a Instagram a ranar 15 ga Yuli, 2022, Dawayya ta ce samun Afakallah da ta yi a matsayin miji, Allah ne ya amsa addu’ar ta.
Dawayya ta ce, “Samun masoyi na gaskiya a wannan zamanin da rashin gaskiya ya yi yawa sai ƙarfin addu’a.
Alhamdu lillahi ya Rabbi lakal hamdu wash shukhur.
Allah na gode maka da ka amsa addu’a ta. Khairun nas man yanfa’un nas.”
Alfijr Labarai
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Fim Magazine